Qin Gang ya fadi haka ne a yayin taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta shirya a wannan rana.
Taron baje-koli na Shanghai zai zama taron baje-koli na farko da kasar Koriyar ta arewa za ta halarta. Bisa labarin da aka samu, an ce, yanzu, kasar Koriya ta arewa ta riga ta share fagen halartar taron, kuma an kusan kawo karshen aikin giggina dakuna da filaye na kasar Koriya ta arewa. Nan ba da dadewa ba, za a gudanar da aikin gwaji. Babban taken kasar Koriya ta arewa a gun taron baje-koli na Shanghai, shi ne "Raya birnin Pyangyong mai wadata, bisa al'adu na kogin Taedong-Gang".(Bako)