in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya yi shawarwari tare da shugaban kwamitin kula da harkokin jihohin kasar Afirka ta kudu
2010-03-30 09:23:27 cri

A ran 29 ga wata, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya yi shawarwari tare da shugaban kwamitin kula da harkokin jihohin kasar Afirka ta kudu Mninwa Mahlangu a birnin Cape Town.

Jia Qinglin ya bayyana cewa, a wasu shekaru da suka gabata, an samu sabon ci gaba kan dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da ta Afirka ta kudu, kasashen biyu sun samu kyakkyawar fahimta da juna da nuna goyon baya ga manyan batutuwan da suke shafar babbar moriyarsu, kuma sun yi hadin gwiwa da taimaka wa juna kan harkokin duniya da na yankuna. Kasar Afirka ta kudu za ta shirya gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya a karo na farko a cikin tarihin nahiyar Afirka. Kasar Sin ta yi imani da cewa, kasar Afirka ta kudu za ta gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya cikin nasara.

Jia Qinglin ya ce, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan ayyukan da aka gudanar bayan taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a karo na 4, kana tana son yin shawarwari tare da kasashen Afirka kamar kasar Afirka ta kudu wajen aiwatar da ayyukan da aka tsara a taron don ba da taimako ga kasashen Afirka wajen tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, da kuma sa kaimi gare su wajen samun bunkasuwa mai dorewa.

Mr Mahlangu ya ce, kasar Afirka ta kudu tana kokarin inganta dangantakar abokantaka tsakaninta da kasar Sin, kana za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak. Kuma yana fatan bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai na kasar Sin zai samu nasara.

Mr Mahlangu ya nuna yabo ga dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da ya taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa hadin gwiwarsu, ya bayyana cewa, kasar Afirka ta kudu za ta yi hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen ba da gudummawa kan gudanar da ayyukan da taron ministoci na dandalin a karo na 4 ya tsara da kuma inganta hadin gwiwarsu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China