in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya isa birnin Cape Town domin ziyarar aiki a kasar Afrika ta kudu
2010-03-29 10:22:59 cri

A ran 28 ga wata, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya isa birnin Cape Town domin ziyarar aiki ta sada zumunta a kasar Afrika ta kudu bisa gayyatar da kwamitin harkokin jihohi na kasar ya yi masa.

Jia Qinglin ya bayar da jawabi a rubuce a filin saukar jiragen saman kasar, inda ya ce, tun daga shekarar 1998 da aka kafa huldar diplomasiyya dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu, huldarsu ta samu bunkasuwa cikin sauri a dukkan fannoni, bangarorin biyu sun kafa huldar abokantaka ta kawo moriyar juna da neman bunkasuwa tare, sun kara amincewa da juna a fannin siyasa, haka kuma, sun samu sakamako da yawa a fannonin tattalin arziki da ciniki da al'adu da tarbiyya da kimiyya da fasaha da kuma yawon shakatawa da dai sauransu, sannan kuma, sun kara yin hadin gwiwa kan harkokin shiyya-shiyya da na duniya.

Jia Qinglin ya ce, kasashen Sin da Afrika ta kudu manyan kasashe masu tasowa ne, inganta da raya huldar dake tsakaninsu ya dace da moriyar jama'ar kasashen biyu, kuma ya ba da gundummawa ga shimfida zaman lafiya a yankuna da kuma duk fadin duniya. An yi imani da cewa, ziyarar da Jia Qinglin ya yi za ta cimma burin kara fahimtar juna da kara samun ra'ayi daya da inganta musanyar ra'ayi da karfafa hadin gwiwa da kuma raya huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China