Jia Qinglin ya yi jawabi a filin jiragen sama, inda ya fadi cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu a shekara ta 1998, ana raya dangantakar da ke tsakaninsu cikin sauri. Bangarorin biyu sun tabbatar da kulla dangantakar abokantaka don zaman daidai wa daidai da moriyar juna kana da samun bunkasuwa tare bisa manyan tsare-tsare, kuma suna karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa. Haka kuma sun samu sakamako mai kyau wajen hadin kansu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu da ilmi da kimiyya da fasaha kana da yawon shakatawa, kuma suna ta inganta hadin gwiwarsu a cikin al'amuran duniya da na shiyya-shiyya.
Haka kuma Jia Qinglin ya furta cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu muhimman kasashe masu tasowa ne. Don haka ba kawai inganta dangantakarsu na dacewa da babbar moriyar kasashen biyu da jama'ar kasashen biyu ba, har ma zai ba da taimako wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwar duniya gaba daya.(Kande Gao)