in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinlin ya gana da shugaban kasar Namibia
2010-03-28 16:05:32 cri

A ranar 26 ga wata a birnin Windhoek, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Jia Qinglin ya gana da shugaban kasar Namibia, Hifikepunye Pohamba, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashen Sin da Namibia, kasashen biyu sun samu sakamako sosai a yunkurin hadin gwiwa a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kuma al'adu, da dai sauransu. Ko da yaushe kasashen biyu suna nuna fahimta ga junansu, da nuna goyon baya ga junansu kan muhimman batutuwan dake da nasaba da moriyarsu.

Bayan haka kuma, Jia Qinglin ya gabatar da shawarwari a fannoni hudu, don inganta dangantakar hadin gwiwa ta abokantaka tsakanin kasashen Sin da Namibia, ciki har da kara amincewa da juna a fannin siyasa, da karfafa hadin gwiwa irin na samun moriyar juna, da kara yin cudanya da hadin kai tsakaninsu a fannin al'adu, da kuma kara daidaita da hada kai kan harkokin duniya, domin neman kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, Mr. Pohamba ya yi godiya ga taimako da goyon baya da kasar Sin ke bayar ga kasar Namibia na tsawon lokaci a fannonin 'yantar da al'umma, da aikin raya kasa. Ya kara bayyana cewa, zai yi kokari tare da kasar Sin domin kyautata yunkurin inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni.

A wannan rana kuma, Mr. Jia Qinglin ya gana da tsohon aminin kasar Sin, kuma tsohon shugaban kasar Namibia wanda ya kafa kasar, Sam Nujoma, inda mutanen biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan kara raya dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Dadin dadawa, a ranar 26 ga wata da dare, Jia Qinglin, da Nujoma, da Asser Kapere, shugaban kwamitin tsarin habaka kasar Namibia sun halarci taron liyafa da aka shirya a birnin Windhoek, don murnar cika shekaru 20 da kulla huldar diplomasiya tsakanin kasashen Sin da Namibia. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China