in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin Jia Qinglin da Asser Kapere
2010-03-26 09:41:49 cri

A ranar 25 ga wata a birnin Windhoek, Mr Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC ya gana da Asser Kapere, shugaban kwamitin tsarin habaka kasar Namibiya.

Mr Jia Qinglin ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan ta yi kokari tare da Namibiya domin kara inganta hadin gwiwa ta sada zumunci tsakanin kasashen biyu ta fannoni hudu, wato kara yin musaya da amincewa juna ta fuskar siyasa, da habaka hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya domin neman samun moriyar juna, da kara yin mu'amala tsakanin jama'ar kasashen biyu ta yadda za a inganta dangantakar sada zumunci dake tsakaninsu, da kuma kara yin hadin kai ta fuskar harkokin duniya da shiyya-shiyya domin kiyaye moriyar bai daya na kasashe masu tasowa.

Kapere ya nuna maraba kwarai da gaske ga zuwan Mr Jia Qinglin, kuma ya ce, yana fatan za a kara bunkasa dangantakar sada zumunci dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. Kasar Sin aminiya ce ga kasar Namibiya. Tun lokacin da kasashen biyu suka kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, sun nuna wa juna goyon baya ta fuskar siyasa, ban da wannan kuma sun kara yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, abubuwan da suka sa dangantakar dake tsakaninsu ta kara bunkasuwa. Hakan ya sa, kasar Namibiya take son yin kokari tare da kasar Sin domin ingiza dangantakar dake tsakaninsu.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China