in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya isa kasar Namibiya don fara ziyarar aiki
2010-03-25 22:41:23 cri

A ranar Alhamis 25 ga watan Maris Mr. Jia Qinlin ya sauka a birnin Windhoek don fara wata ziyarar aiki a kasar Namibiya dake a kudu maso yammacin Afirka.

Jia Qinglin wanda shi ne shugaban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, yana wannan ziyara ne bayan daya samun goron gayyata daga majalisar dokoki ta kasar Namibiya.

A ziyarar tasa ta tsawon kwanaki goma dai a Afirka, kasar ta Namibiya ita ce zangonsa na biyu, bayan kasar Kamaru. Har ila yau yayin wannan ziyara a makon gobe ne zai isa kasar Afirka ta kudu.

A cikin wata takardar jawabi da ya bayar bayan isarsa filin jiragen saman Namibiyar ya bayyana kasar da cewar ita ce 'yar autar Afirka da ta samu cikakken 'yancin kai a shekarar 1990, kana ta kasance mai cikakken kuzari.

Mr. Jia ya ce wannan ziyara tasa tana da nufin bunkasa fahimtar juna da kulla aminci a tsakanin kasashen biyu, gami da kokari tabbatar da dorewar hakan ta ko wane bangare.

A yayin ziyarar tasa a Namibiya zai gana da shugabannin kasar gami da halartar bikin cika shekaru 20 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Namibiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China