in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin raya kananan masana'antu
2010-03-25 21:40:20 cri
Jama'a masu karatu, mai yiyuwa ne ka gano cewa, a cikin dimbin kayayyakin da kake amfani da su a yau da kullum, galibinsu, kamar na'urorin rediyo da tangarau da tawul, kayayyaki ne da aka shigo da su daga kasar Sin. Kuma su kayayyaki ne da aka yi a matsakaita da kananan masana'antun kasar Sin. Yanzu, irin wadannan masana'antu sun riga sun zama madogara wajen bunkasa tattalin arziki da kirkiro sabbin fasahohi da kuma samar da guraban aikin yi.

Bisa kididdigar da aka yi, yawan GDP da matsakaita da kananan masana'antun da yawansu ya kai kimanin miliyan 50 suka yi ya kai kimanin kashi 60 cikin kashi dari, kuma yawan harajin da suka samar ya kuma kai rabin jimillar harajin da kasar Sin ta saka. A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a kwanan baya, Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya nuna cewa, "Za a kara tallafawa matsakaita da kananan masana'antu da kara hanyoyin hada-hadar kudi da za su iya bi domin warware matsalolin da suke fuskanta kan batun hada-hadar kudi. Sannan za a ci gaba da aiwatar da manufofin kasafin kudi masu alfarma ga matsakaita da kananan masana'antu. Yawan kasafin kudin da gwamnatin tsakiya za ta kebe musu zai kai kudin Sin yuan biliyan 10 da miliyan dari 6 a shekarar 2009."

A ganin Mr. Cui Yongkai wanda ya dade yana tafiyar da wata karamar masana'antar samar da kayayyakin gina gidaje, matakan da firaminista Wen Jiabao ya sanar a cikin rahoton gwamnati albishir ne da yake son samu cikin dogon lokacin da ya gabata. Mr. Cui ya ce, batun hada-hadar kudi wata matsala ce da ke kayyade ci gaban matsakaita da kananan masana'antu. Lokacin da ake farfado da kuma bunkasa tattalin arziki, wannan batu ya tsananta. "Har yanzu matsakaita da kananan masana'antu suna fuskantar matsalar hada-hadar kudi. Ba mu iya samun rancen kudi daga bankunan gwamnati ba sabo da kasancewar sharuda masu tsanani. Yanzu wasu kananan kamfanonin kudi suna ba da rancen kudi, amma dole ne a biya ruwan kudi da yawa. Muna tsoron neman irin wannan rancen kudi."

Yaya za a iya warware matsalar hada-hadar kudi da matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni suke fuskanta? Mr. Zhao Xiaoyong wanda yake aiki a kungiyar kula da harkokin masana'antu da kasuwanci masu zaman kansu ta kasar Sin ya ba da shawara cewa, "A ganina, ya kamata kamfanonin inshora na gwamnati su shiga aikin ba da rancen kudi ga matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni sabo da kwarewarsu da karfinsu suna iya ba da gudummawa sosai wajen tallafawa matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni. Shawarata ita ce, matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni suna iya neman rancen kudi domin wasu shirye-shiryen da suka samu kyauta a matsayin kasar a fannin kimiyya da fasaha. Kuma gwamnatin kasar ta iya ba da lamuni ga irin wadannan shirye-shirye. Sakamakon haka, bankuna za su iya samun tabbaci a lokacin da suke ba da rancen kudi ga matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni."

Yanzu kwamitin sa ido da kula da harkokin bankuna na kasar Sin ya riga ya nemi bankunan kasuwanci na gwamnati da su kafa hukumomin ba da rancen kudi musamman domin kara karfin tallafawa matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni. A kwanan baya, Bankin Huaxia, wani bankin kasuwanci na kasar Sin ya bayar da "shirin kwale-kwalen Dragon" domin matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni. Malama Kang ta wannan banki ta bayyana cewa, "Masana'antu da kamfanoni masu mallakar fasahohin zamani da na tafiyar da kwangilolin gine-gine da na cinikayya suna bukatar dimbin rancen kudi."

Malama Kang ta bayyana cewa, sabo da gwamnati tana sa kaimi ga bankunan kasuwanci da su ba da rancen kudi ga matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni, yanzu yawancin bankuna sun riga sun bayar da manufofin samar musu rancen kudi.

A hakika dai, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin tana nuna wa matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni goyon baya a fannin hada-hadar kudi ba, har ma tana ci gaba da kebe kasafin kudi domin tallafawarsu. Mr. Zhao Xiaoyong ya bayyana cewa, "Gwamnatin tsakiya ta kan kebe kasafin kudi domin tallafawa wasu masana'antu da kamfanoni ba tare da karbar ruwa ba. Ma'aikatar kudi da ma'aikatar kula da masana'antu da sadarwa da kwamitin neman ci gaba da yin kwaskwarima na kasar Sin su kan kebe irin wannan kasafin kudi tare."

Haka kuma, Mr. Li Yizhong, ministan kula da masana'antu da sadarwa na kasar Sin ya bayyana a kwanan baya a nan birnin Beijing, cewar gwamnatin kasar za ta dauki matakai iri iri domin tallafawa matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni wajen neman ci gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China