in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya kai ziyara a kwalejin Confucius dake kasar Kameru
2010-03-25 14:55:33 cri

A ran 24 ga wata da yamma, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin dake ziyara da sada zumunta a kasar Kameru a hukunce ya kai ziyara a kwalejin Confucius na jami'ar Yaounde ta biyu, domin jinjinawa wasu daliban Kameru dake koyon Sinanci a can.

Wasu kayayyaki irin na karamawa na al'adun gargajiyar kasar Sin masu launin ja da ake kira Zhongguojie, da abubuwan rufe fuska da a kan yi amfani da su musamman a cikin wasannin kwaikwayo na al'adun gargajiyar kasar Sin mai suna Beijing Opera, da tutar Sin da ta Kameru, dukkansu sun bayyana al'adun kasar Sin, tare da dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. A ran 24 ga wata da yamma, ana farin ciki sosai a kwalejin Confucius na jami'a ta biyu ta birnin Yaounde, hedkwatar kasar Kameru. Malamai da dalibai na wannan kwaleji da mutane masu sada zumunta na sassan daban daban kimanin 400 suna maraba da baki daga kasar Sin. "Assalamu alaikum! Malam Jia Qinglin, barka da zuwanka a kwalejin Confucius!"

A wannan rana da yamma, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin Jia Qinglin dake ziyara da sada zumunta a kasar Kameru ya kai ziyara ta musamman a kwalejin Confucius na jami'ar Yaounde ta biyu domin jinjinawa malamai da dalibai a can.

An kafa wannan kwalejin Confucius a watan Nuwamba na shekarar 2007, wanda yake kunshe da dalibai sama da 2400. Kasar Kameru ta mayar da shi a matsayin wani abin koyi a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na duniya. A shekarar 2009, ofishin kula da Sinanci na kasar Sin ya nuna yabo ga wannan kwalejin Confucius.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China