in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya gana da shugaban kasar Kamaru
2010-03-24 22:34:04 cri
A ran 24 ga wata, Mr. Jia Qinglin, shugaban zaunnanen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya gana da shugaban kasar Kamaru Paul Biya a Younde, inda da farko ya mika godiya ga shugaba Paul Biya da gwamnatin kasar Kamaru bisa kokarin da suka nuna wajen ceton masunta 7 na kasar Sin wadanda aka sace su a yankin tekun Kamaru a kwanan baya.

Jia Qinglin ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen gudanar da alkawuran daukar sabbin matakai 8 na kara raya huldar da ke tsakaninta da kasashen Afirka. Kuma kasar Sin tana son kara yin cudanya da shawarwari da dukkan kasashen Afirka, ciki har da kasar Kamaru domin sauraran shawarwarinsu. Kuma za a aiwatar da wadannan matakai 8 a kai a kai bisa hakikanin bukatun da kasashen Afirka suke da su domin moriyar jama'ar kasashen Afirka cikin sauri.

A  nasa bangaren, Mr. Paul Biya ya amince da ra'ayin da Mr. Jia Qinglin ya gabatar domin ci gaba da raya huldar da ke kasancewa a tsakanin kasashen Kamaru da Sin. Kuma ya bayyana cewa, kasarta za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufar Sin daya tak a duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China