in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Kamaru
2010-03-24 14:48:34 cri
A ran 23 ga wata da karfe 4 da minti 40 na yamma agogon kasar Kamaru, babban dakin taro na majalisar dokokin kasar ya cika makil da mutane fiye da 400, ciki har da dukkan 'yan majalisar dokoki da 'yan majalisar ministoci da kwararru da masana na Kamaru kana da jakadun kasashe daban daban da ke kasar, domin saurarar jawabin da Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya yi. Jia Qinglin ya bayyana cewa,

"Kamar yadda 'yan kasar Kamaru su kan ce, abokan arziki 'yan uwa ne. Jama'ar kasar Kamaru aminai ne na jama'ar Sin. A cikin shekaru kusan 40 da suka gabata bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Kamaru, shugabannin kasashen biyu sun dora matukar muhimmanci kan karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, kuma kasashen biyu sun fuskanci sauye-sauyen duniya tare."

Kasar Kamaru dai tana yammacin yankin da ke tsakiyar Afirka ne. Tun bayan da ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin a watan Maris na shekara ta 1971, ko da yaushe ana karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. A shekara ta 2009, jimillar kudin da aka samu daga cinikayya a tsakaninsu ta kai dala miliyan 810, dimbin ayyukan da jama'a ke amfana da su sun samu bunkasuwa a kasar Kamaru bisa taimakon kasar Sin, ciki har da babban dakin taro, da tashar samar da wutar lantarki ta hanyar karfin ruwa, da asibitin mata da yara, wadanda suka zama alamar kara dangon zumunci a tsakanin kasar Sin da Kamaru.

Bayan abkuwar matsalar kudi ta duniya, ko da yake kasar Sin ta gamu da manyan wahalhalu ta fuskar tattalin arziki, amma tana kara samar da taimako ga Afirka gwargwadon karfinta. A yayin taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afirka, gwamnatin kasar Sin ta sanar da sabbin matakai takwas don inganta hadin kansu.

Hadin kan Sin da Afirka ya jawo hankalin duk duniya, wasu ba su fahimci sabbin matakan sosai ba, wasu kuma suna shakkarsu. Game da sirrin inganta hadin kan kasar Sin da Afirka, kuma Jia Qinglin ya furta a cikin jawabinsa, cewar

"A nan, ina son in gaya muku gaskiya, cewar ko a lokacin da, ko a nan gaba, ko na da yaushe mun mayar da batun karfafa dangantakar hadin kai ta aminci tare da kasashen Afirka a matsayin wani muhimmin sashe na manufar diplomassiya da kasar Sin ke bi domin samun 'yancin kai da zaman lafiya. Haka kuma mu kan tsaya tsayin daka kan bin ka'idojin zaman daidai wa daida, da moriyar juna, da daukar hakikanin matakai, kana da bude kofa, wannan shi ne sirrin ingantuwar hadin kan Sin da Afirka."

Sakamakon hadin kan Sin da Afirka a cikin rabin karnin da ya gabata, Sin ita ma ta samu manyan nasarori ta fuskar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Jia Qinglin ya furta cewa, Sin za ta samar da taimako ga kasashe masu tasowa yayin da take kokari samun bunkasuwa. Ya ce,

"bayan da kasar Sin ta samu bunkasuwa, za ta budewa kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka hanyoyi daban daban, da kuma kara sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Bayan da kasar Sin ta samu bunkasuwa, za ta kara karfin dukkan kasashe masu tasowa domin kiyaye moriyarsu gaba daya. Haka kuma bayan da kasar Sin ta samu bunkasuwa, za ta nuna himma da kwazo wajen samun zaman lafiya da bunkasuwar duniya, da kuma bayar da babbar gudummowa ga ci gaban bil Adam."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China