in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar wakilai ta kasar Kamaru
2010-03-24 10:59:06 cri

A ran 23 ga wata, a birnin Yaounde, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Jia Qinglin ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar wakilai ta kasar Kamaru Cavaye Yeguie Djibril.

Jia Qinglin ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna babban yabo ga kasar Kamaru da ta nacewa ga bin manufar Sin daya tak a duniya da nuna goyon baya ga kasar Sin a kan batutuwa da ke shafi moriyar kasar Sin. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da Kamaru a fannin aiwatar da sabbin matakai 8 na inganta hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka tsara a kan taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin kasar Sin da Afirka, don tabbatar da bunkasuwa tare.

Cavaye Yeguie Djibril ya bayyana cewa, kasar Kamaru za ta ci gaba da nacewa ga bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma majalisar wakilai ta kasar Cameroon za ta ci gaba da kara yin mu'amala da yin hadin gwiwa tare da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin. Kasar Kamaru tana son yin kokari tare da Sin wajen sa kaimi ga karfafa dankon zumunci a tsakaninsu, da kawo moriyar jama'ar kasashen biyu.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China