in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya yi jawabi a majalisar wakilai ta kasar Cameroon
2010-03-24 09:31:13 cri

A ran 23 ga wata, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Jia Qinglin ya yi jawabi a majalisar wakilan ta kasar Cameroon mai taken "za a karfafa dankon zumunci a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka". Dukkan membobin majalisar wakilan kasar Cameroon da membobin majalisar ministoci da masana da kwararru da jakadun kasa da kasa da ke kasar Cameroon da yawansu ya wuce 400 sun halarci taron.

Jia Qinglin ya bayyana cewa, sabbin matakai 8 na inganta hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun shaida zumuncin da jama'ar kasar Sin ke nunawa al'ummar nahiyar Afirka, kuma ya kamata wadannan matakai su sa kaimi ga kara karfin kasashen Afirka a fannin bunkasuwar kansu, da cimma makasudin samun bunkasuwa na shekarar dubu biyu na M.D.D ba tare da bata lokaci ba.Ban da haka kuma, Jia Qinglin ya jaddada cewa, bunkasuwar da kasar Sin ta samu zai kara kawo moriya ga kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da ke tsakanin kasashe masu tasowa, da kara karfin kasashe masu tasowa, da kiyaye moriyar wadannan kasashe, da sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya a duniya, da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar wayewar kai na Dan Adam.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China