in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya tashi daga birnin Beijing don kai ziyara a kasashe 3 na Afrika
2010-03-21 16:57:18 cri

A ran 21 ga wata da safe, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasashen Kamaru da Namibia da kuma Afrika ta kudu don kai ziyarar sada zumunci.

Jia Qinglin ya yi wannan ziyara ne bisa gayyatar da majalisar wakilan kasar Kamaru da majalisar dokoki ta kasar Namibia da kwamitin harkokin jihohi na kasar Afrika ta kudu suka yi masa. Wannan ne karo na farko da shugabannin kasar Sin suka kai ziyara a kasashen Afrika a wannan shekara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China