in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar People's Daily ta rubuta bayanin edita domin taya murnar kammala taro na cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin
2010-03-15 14:24:13 cri
A ranar 15 ga wata, jaridar People's daily ta rubuta bayanin edita, domin taya murnar kammala taro na cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin da cikakkiyar nasara.

A cikin bayanin edita, an bayyana cewa, wannan taro ya kasance wani muhimmin taron da aka yi, yayin da kasar Sin ke warwarewa daga rikicin kudi na duniya, da tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki da lafiya da gaggauta canja salon samun bunkasuwar kasar Sin. An yi wannan taro ne cikin tsarin demokuradiyya da hadin gwiwa da nuna gaskiya.

A cikin bayanin edita, an ce, a gun taron, an zartas da gyararren shirin dokokin zabe na kasar, kuma za a gudanar da zaben wakilan majalisar wakilan jama'a a daidai gwargwado da yawan mutane a birane da kauyuka. Aikin yin gyare-gyare ga dokokin zabe, ya kasance wani babban ci gaban siyasar demukuradiyya mai zaman gurguzu na kasar Sin, kuma ya zama babban ci gaban hakkin kiyaye harkokin dan Adam.

A cikin bayanin edita, an ce, game da yanayin duniya mai sarkakiya da ake ciki, yayin da ake fuskantar kalubale da dama, ana bukatar tsarin majalisar wakilan jama'a da ya kara taka muhimmiyar rawa da ba da fifiko, da yin kokari tare, domin kara kwarin gwiwar jama'a, da ciyar da manyan ayyukan kasar Sin gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China