in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na kasashen waje sun dora muhimmanci sosai kan taron manema labaru da Firaministan Sin Wen Jiabao ya yi
2010-03-15 12:55:13 cri

A ranar 14 ga wata, a nan birnin Beijing, an kammala taro na cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin. Yayin da kafofin yada labaru na kasashen waje ke ba da rahotanni game da bikin kammala taron, sun dora muhimmanci sosai kan jawabin da firaministan Sin Wen Jiabao ya yi a gun taron manema labaru.

Kamfanin dillancin labaru na AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa, a ranar 14 ga wata, an kammala taron majalisar wakilan jama'a, inda aka zartas da daftarin shiri na kasafin kudin kasar na shekarar 2010, a cikin daftarin, an sake jaddada cewa za a kara kebe kudade domin aikin jinya da ilmi da gina gidajen kwana a kan farashi mai rahusa ga matalauta.

Kamfanin dillancin labaru na Amurka AP ya bayyana cewa, a gun taron manema labaru, firaministan Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, sabo da kasancewar mutane da yawa da suka rasa aikinsu a cikin gamayyar tattalin arziki ta duniya, ana ci gaba da samun hadari a cikin tsarin kudi na duniya, mai yiwuwa ne tattalin arzikin duniya zai samu koma baya a karo na biyu. Yayin da ake bayyana tattalin arzikin Sin, Mr. Wen ya ce, manyan masana'antun Sin da dama ba su samu kyautatuwa, ya zuwa yanzu suna dogoro kan manufar da gwamnatin Sin ke bayarwa.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya yi sharhi cewa, a gun taron manema labaru, Mr. wen ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga yunkurin yin gyare-gyare ga tsarin darajar musayar kudin RMB yadda ya kamata, matsin lamba da kasashen duniya suka yi wa kasar Sin ba zai kasancewa mai amfani ga kasar Sin, domin yin gyare-gyare ga kan darajar musayar kudin RMB ba.

A cikin bayanin da Jaridar Wall Street Journal ta yi a shafinta na Internet, an ce, Mr. Wen ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza aikin yin gyare-gyare ga tsarin tattalin arziki da siyasa da dai sauran fannoni, kuma ya ce, shimfida adalci da zaman daidaito a zamantakewar al'umma zai kafa tushe domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China