Wen Jiabao ya furta cewa, ko da yake kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar tattalin arziki a 'yan shekarun da suka gabata, amma sakamakon rashin samun daidaito a tsakanin birane da yankunan karkara, da kuma tsakanin wurare daban daban, kana da samun yawan mutane da tushen tattalin arziki maras inganci, za a kwashe shekaru 100 ko fiye in kasar Sin tana son kaiwa matsayin zamanintarwa.
Haka kuma Mr. Wen ya jaddada cewa, Sin ta nace ga bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana. A matsayinta ta wata kasa da ke daukar alhaki a kai, Sin tana tsayawa kan ra'ayin inganta hadin kai tare da kasa da kasa cikin yakini domin warware manyan batutuwan da ke gaban duniya a fannonin tattalin arziki da siyasa. Sin tana samar da taimako ga kasashe masu fama da talauci ne ba tare da ko wane sharadi ba.(Kande Gao)