A cikin taron shekara shekara na NPC na bana, ajanda daya tak da ba a saba yi ba ita ce tattaunawar gyararren daftarin dokar zabe. Yayin da aka kada kuri'a kan daftarin a bikin rufe taron, an amince da shi bisa kuri'u masu dimbin yawa. Don haka, mazauna yankunan karkara da na birane na kasar Sin za su iya zabar wakilan jama'a bisa kason jama'a daya.
Wu Bangguo, shugaban majalisar NPC ya bayyana a gun bikin rufe taron, cewar zabar wakilan jama'a cikin yankunan karkara da birane bisa kason jama'a daya ya dace da hakikanin halin da kasar Sin ke ciki, da kuma moriya daya ta 'yan kabilu daban daban. Kana ya iya sheda ka'idar samun daidai wa daida a tsakanin kowa da kowa da yankuna daban daban da kuma kabilu daban daban. Bugu da kari kuma wannan zai taka muhimmiyar rawa ga nacewa kan kyautata tsarin majalisar NPC da kuma raya siyasar gurguzu irin ta dimokuradiyya.(Kande Gao)