Wen Jiabao ya gana da manema labarun gida da na waje bayan da aka rufe taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda ya furta cewa, batun sauyawar yanayi yana da nasaba da kasancewar bil Adam a duniya, da muradun kasashe daban daban, kana da samun daidai wa daida da adalci a duniya. Ka'idar "daukar nauyi tare amma akwai bambanci" da kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kai ta yi daidai sosai, kasar Sin kuma za ta ci gaba da hadin kai tare da kasashen duniya domin sa kaimi ga yunkurin tinkarar sauyawar yanayi.
Ban da wannan kuma, Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da wani kyakkyawan muhalli ga kamfanonin waje bisa doka ta yadda za su iya raya ayyukansu cikin daidai wa daida, da kuma more gata ta musamman kamar yadda kamfanonin kasar Sin ke yi. (Kande Gao)