Yayin da Wang Zhiguo ke zantawa da manema labaru a cibiyar yada labaru a yayin taro na cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya ce, ana gudanar da aikin zirga-zirgar jiragen kasan da suka fi sauri cikin armashi, watau na farko, ana tabbatar da ingancin nau'rori. Na biyu kuwa, ana yin zirga-zirga lamin lafiya, ba tare da jikkata ko mutuwar fasinjoji ba, na uku, ana gudanar da zirga-zirgar jiragen kasa yadda ya kamata.(Bako)