in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan jama'a sun gabatar da shirye-shirye 506 a yayin taron majalisar wakilan jama'ar Sin na wannan shekara
2010-03-13 20:26:51 cri

A ran 13 ga wata, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Mr.Kong Ping, mataimakin shugaban sashen kula da shirye-shirye na sakatariyar taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, a yayin taron, gaba daya wakilan sun gabatar da shirye-shiryen da yawansu ya kai 506.

Mr.Kong Ping ya kara da cewa, shirye-shiryen da wakilan suka gabatar sun shafi fannonin tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'umma da sauransu. Yanzu haka dai, an riga an gabatar da shirye-shiryen zuwa sashe na musamman na majalisar wakilan jama'ar Sin don a yi nazari a kansu.

Baya ga shirye-shiryen da wakilan suka gabatar a gun taron, wakilan sun kuma gabatar da shawarwarin da suka shafi ci gaban kasa da batutuwan da suka jawo hankalin jama'a.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China