Panchan Lama na 11 Erdeni Qoigyi Gyaibo, jagoran addinin Buddha a jihar Tibet da ya bayyana a dandalin siyasa na kasar Sin a karo na farko shi ne sabon jini da ya jawo hankali sosai a yayin taron a shekarar da muke ciki. Panchan mai shekaru 20 a duniya ya zama mamban majalisar CPPCC a watan Febrairun bana. A game da kulawar da aka nuna masa, ba tare da nuna girman kai ba ya bayyana cikin nitsuwa cewa,"Na koyi dimbin sabbin abubuwa a sakamakon halartar taron a wannan shekara. Na gane wa idona yadda mambobin majalisar sun ba da shawarwari, sun tattauna da kuma shiga cikin harkokin kasa. Sun ba da shawarwari da zummar ganin jam'iyyarmu da gwamnatinmu sun kara bauta wa jama'a yadda ya kamata. Ni ne sabon jini, ina bukatar ci gaba da kokari."
A lokacin da yake tattaunawa da wasu mambobin majalisar da suka fito daga rukunin addini, Panchan ya yi bayani kan ra'ayinsa na sauke nauyinsa a matsayin mamban majalisar CPPCC ta hanyar da ta dace.