in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na nuna tsayayyiyar kin amincewa ga kowace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin gidanta bisa batun hakkin dan Adam, in ji kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar
2010-03-13 18:17:10 cri

A game da rahoton da Amurka ta bayar kan halin hakkin dan Adam a kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Qin Gang ya bayyana a ran 12 ga wata cewa, Sin na nuna tsayayyiyar kin amincewa ga kowace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin gidanta bisa batun hakkin dan Adam.

A ran 11 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta bayar da rahoto kan hakkin bil Adam na kasa da kasa cikin shekarar 2009, idan ta sake yin suka a kan yadda Sin ke kula da hakkin bil Adam. A game da hakan, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na dora matukar muhimmanci a kan kiyaye hakkin bil Adam da tattala shi. Tsarin mulki na kasar da dokokinta duk suna tabbatar da hakkin bil Adam. Baya ga haka, a cikin shekaru 31 da suka wuce bayan da aka fara aiwatar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin kasar Sin ya yi ta bunkasa, harkokin dimokuradiyya da dokoki ma sun samu ci gaba sosai, ana kuma tabbatar da 'yancin jama'a na bin addini, jama'ar Sin na kabilu daban daban suna samun cikakken 'yanci da hakki, wannan abu ne da kowa ya gani.

Qin Gang ya kara da cewa, Sin na son yin musanyar ra'ayoyi tare da kasa da kasa kan hakkin bil Adam bisa tushen zama daidai wa daida da girmama juna, amma tana tsayawa tsayin daka ga kowace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin gidanta bisa batun hakkin bil Adam. Sin tana bukatar Amurka da ta duba hakkin bil Adam na kanta, kar ta dauki kanta a matsayin "makarin hakkin bil Adam", kuma ta daina bayar da rahotanni kan hakkin bil Adam na kasa da kasa kan yunkurin tsoma baki cikin harkokin gida na saura.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China