in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai domin bunkasa harkokin sayayya a bana
2010-03-13 17:43:16 cri

A ranar 13 ga wata, mai ba da taimako ga ministan kasuwanci na kasar Sin Fang Aiqing ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, za a ci gaba da daukar matakai domin bunkasa harkokin sayayya a bana, da kokarin samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar kara yawan sayayya.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Fang Aiqing ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta sami sakamako mai kyau wajen kara yawan hada-hadar kudi da yin sayayya. A bana, za a ci gaba da daukar matakai habaka bukatu a gida, musamman ma za a yi kokari wajen bunkasa harkokin sayayya. Matakan da za a dauka za su hada da kara yin sayayya wajen manyan batutuwa, watau za a yi kokari wajen sa kaimi kan sayen sayayyar motoci da kayayyakin zamani da ake amfani yau da kullum, da kara raya harkokin sayayya a kauyuka, da kyautata tsarin ba da hidima game da zaman rayuwar jama'a a birane, da kashe karin kudi domin samun hidima, da kara samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ko fitar da hayakin Carbon ba, da kara yin sayayya kan kayayyakin da za a sake yin amfani da su, da inganta tsarin ba da kudin rance wajen hada-hadar kudi da ba da inshora, da kara yawan sayayya wajen ba da rance.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China