in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na CPPCC
2010-03-13 17:20:32 cri

Ranar 13 ga wata da safe, a nan birnin Beijing, an rufe taro na uku na kwamiti a karo na 11 na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, inda manyan shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin, da shugabannin kasar suka halarci bukin rufe taron, ciki kuwa har da shugaban kasar Sin Hu Jintao, da shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Wu Bangguo, da firaminista Wen Jiabao, da shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa Jia Qinglin.

A yayin bukin rufe taron, Mista Jia Qinglin ya gabatar da jawabin cewa, a yayin taron da aka yi a wannan karo, membobi sun mayar da hankali sosai kan batutuwa da dama, ciki har da kokarin gaggauta kawo sauyi ga hanyar da ake bi wajen raya tattalin arziki, da yadda za'a yi domin bunkasa tattalin arziki cikin sauri kuma yadda ya kamata, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da yin gyare-gyare kan muhimman sana'o'i, tare kuma da kara bude kofa ga kasashen waje. Haka kuma, membobin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa sun yi kokarin bada shawarwari a game da yadda za'a samu bunkasuwa bisa kimiyya, wadanda kuma suka taka muhimmiyar rawa a fannin bada shawarwari ga yunkurin yanke shawara kan muhimman batutuwa.

Mista Jia ya ci gaba da cewa, kamata ya yi a mayar da hankali kan kokarin kawo sauyi ga hanyar da ake bi wajen neman bunkasuwar tattalin arziki a yayin da ake gudanar da harkokin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa a wannan shekara, da kara yin nazari, da bayar da kyawawan shawarwari game da raya tattalin arziki yadda ya kamata kuma cikin sauri. Har wa yau, ya kamata a kara dora muhimmanci kan batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'a, ciki har da samar da guraban ayyukan yi, da ayyukan bada ilimi, da na jinya, da harkokin kiyaye muhalli, da sauran makamantansu, tare kuma da karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin jama'ar babban yankin kasar Sin da na yankunan Hongkong, da Macau, da Taiwan.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China