in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'yan majalisar CPPCC da suka fito daga bangaren addini sun yi watsi da takardar bayani kan hakkin bil Adam da Amurka ta bayar
2010-03-12 21:20:59 cri

A ran 11 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ta bayar da takardar bayani kan hakkin bil Adam na kasa da kasa ta shekarar 2009, inda a cewarta, Sin ta danne wa 'yan kananan kabilu da ke jihohin Tibet da Xinjiang 'yancin bin addininsu da al'adunsu, bayanin da ya jawo suka daga 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin da suka fito daga bangarorin kananan kabilu da na addini.

Lhakpa Phuntsok, dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin kuma babban darektan cibiyar nazarin al'adun Tibet, ya ce, ya taba zuwa kasashe da shiyyoyi fiye da 40, amma bai taba gane wa idonsa wurin da ke da yanayin addini mai kyau da ya kai na Tibet ba, bayanin da ya bambanta da wanda Dalai Lama ya yi.

Lhakpa Phuntsok ya kara da cewa, takardar da Amurka ta bayar ba ta da madogara. Kowace shekara, yana zuwa Tibet inda ya kan shafe tsawon watanni biyu yana nazari, inda kuma ya gane wa idonsa yadda zaman rayuwar jama'ar Tibet ke dinga kyautatuwa, da kuma yadda ake tattala wa jama'ar wurin 'yancinsu na bin addininsu. A ganinsa, kamata ya yi mutanen yammaci su je Tibet su gani da idonsu kafin su yi bayani.

Bayan haka, Bekly Mamut, wani dan majalisar, wanda shi ne jagoran addinin musulunci a gundumar Shanshan ta jihar Xinjiang, ya ce, musulmai na Xinjiang suna iya zuwa masallaci su yi salla yadda suka ga dama, haka kuma suna iya azumi cikin watan Ramadan cikin 'yanci. Bayan haka, kowace shekara, gwamnati na tura musulmai dubu 12 zuwa Makka domin aikin Hajji.

Bekly Mamut ya jaddada cewa, dokokin kasar Sin na tabbatar da 'yancin jama'a na bin addini, zance na wai "an danne wa kananan kabilu na jihar Xinjiang 'yancin bin addininsu da al'adunsu", bai dace da hakikanin gaskiyar da ke kasa ba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China