in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a yi kokarin samun bunkasuwa da raya sojojin kasa a cikin yunkurin inganta zamantakewar al'umma mai wadata, in ji Hu Jintao
2010-03-12 20:23:13 cri

A ranar 12 ga wata, bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya jaddada a nan birnin Beijing cewa, kamata ya yi a yi kokarin samun bunkasuwa da raya sojojin kasa yayin da ake kokarin inganta zamantakewar al'umma mai wadata daga dukkan fannoni.

A wannan rana, Hu Jintao ya halarci taro na tawagogin sojoji na cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'a a karo na 11, kuma bayan da ya saurari jawaban da wakilai suka yi, ya bayyana cewa, ya zama dole a fahimta da yin amfani da sauyawar yanayin tsaro da ake ciki, da inganta ra'ayin tsaron kasa daga dukkan fannoni, da ci gaba da mayar da aikin samun bunkasuwa a matsayin aikin da ke gaban kome, da tsayin daka kan mayar da aikin tsaro da zaman kai gaban kome, da kyautata aikin samun bunkasuwar tattalin arziki da inganta aikin tsaro tare, domin cimma burin samun bunkasuwa da raya sojojin kasar a cikin kokarin inganta zamantakewar al'umma mai wadata daga dukkan fannoni.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China