in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mai da tsarin sa kaimi ga batun samar da ilmi bisa adalci a matsayin babbar manufar kasar a fannin ba da ilmi
2010-03-12 15:18:59 cri

A ran 12 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin ministan kula da harkokin ba da ilmi na kasar Sin Hao Ping ya bayyana cewa, an fara neman ra'ayoyin jama'a kan ka'idojin kasar game da yin kwaskwarima kan aikin ba da ilmi da bunkasuwarsa da za a yi a ran 28 ga watan Febrairu, inda aka jaddada cewa, an mai da tsarin sa kaimi ga batun samar da ilmi bisa adalci a matsayin babbar manufar kasar Sin a fannin ba da ilmi.

A gun taron manema labaru a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Hao Ping ya bayyana cewa, ka'idojin sun dora muhimmanci kan batutuwan zaman rayuwar jama'a, da mai da hankali kan abubuwa masu amfani ga jama'a yayin da ake gudanar da aikin ba da ilmi, da kafa tsarin ba da hidimar ilmi a birane da kauyuka, ta hakan za a tabbatar da cewa dukkan jama'a sun samu ilmi cikin adalci. Ya kamata a samar da kayayyakin inganta ilmi, musamman ga kauyuka da yankuna masu fama da talauci da kuma yankunan kananan kabilu don sa kaimi ga samun bunkasuwar aikin ba da ilmi yadda ya kamata.

Hao Ping ya bayyana cewa, kafin a kammala tsara ka'idojin, an riga an samu ra'ayoyin jama'a miliyan 2.1, kana ana neman matakan da za a dauka don warware matsaloli a cikin ka'ida.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China