in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta kulla yarjejeniyar tsarin tallafawa kasar Sin tare da MDD
2010-03-12 15:05:56 cri

A ran 12 ga wata a nan birnin Beijing, a madadin gwamnatin kasar Sin, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Yi Xiaozhun ya kulla wata yarjejeniyar tsarin tallafawa kasar Sin ta shekarar 2011 zuwa shekarar 2015 ta MDD tare da Khalid Malik, jami'in MDD dake kasar Sin.

Gwamnatin kasar Sin da hukumar MDD dake kasar Sin sun tsara wannan yarjejeniya cikin hadin kai bisa tsarin bunkasuwar kasar Sin da kuma la'akari da fifikon da hukumomin MDD suka nuna. Takartar ta tabbatar da cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin da MDD za su yi hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki marasa gurbata muhalli da taimakawa mutanen da suke fama da talauci da kara yin musanyar ra'ayi a tsakanin kasa da kasa, yarjejeniyar za ta ba da taimako ga MDD wajen yin hadin gwiwa tare da kasar Sin domin neman samun bunkasuwa daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China