in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nemi Dalai Lama da ya dakatar da ra'ayin kawo mata baraka
2010-03-11 21:05:13 cri

A ranar 11 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bukaci Dalai Lama da ya dakatar da ra'ayin kawo wa Sin baraka, domin kafa tushe ga yin shawarwari tsakaninsa da gwamnatin tsakiya.

Qin Gang ya fadi haka ne a gun taron manema labaru da aka saba yi a nan birnin Beijing, ya ce, sanarwar da Dalai ya bayar a ranar 10 ga wata, murde gaskiya ne game da halin da ake ciki a jihar Tibet, kuma hakan ya kawo karan tsaye game da manufar da gwamnatin tsakiya ta bayar kan jihar Tibet, kuma kara yin furofaganda ne kan ra'ayin kawo wa Sin baraka. Qin Gang ya bayyana cewa, yanzu abin da ya kamata Dalai ya yi shi ne da-na-sani game da kuskuren da ya yi da matsayin da yake kai, kuma ya dakatar da ra'ayin kawo wa Sin baraka.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China