in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saurari rahotannin da kotun kolin jama'ar Sin da babbar hukumar kula da harkokin shari'a ta jama'ar kasar suka gabatar dangane da ayyukan da suka yi a bara
2010-03-11 20:01:16 cri

A ran 11 ga wata, an gudanar da cikakken zama a karo na hudu na taron wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi yanzu a nan birnin Beijing, inda aka saurari rahotannin da kotun kolin jama'ar Sin da babbar hukumar kula da harkokin shari'a ta jama'ar kasar suka gabatar dangane da ayyukan da suka yi a shekarar da ta gabata.

Shugabannin kasar Sin, ciki har da Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin sun halarci taron.

A cikin rahotonsa, shugaban kotun kolin jama'ar kasar Sin, Wang Shengjun ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, Sin ta yanke hukunci mai tsanani a kan laifuffukan da suke iya lalata tsaron kasar, kana da laifuffuka na kisan gilla da yin garkuwa da mutum da fasa bom da sauran manyan laifuffuka, kuma gaba daya an yanke hukunci a kan masu laifi da yawansu ya kai dubu 375, wanda ya karu da kashi 0.8% bisa na shekarar bara.

Mr.Wang Junsheng ya kara da cewa, kotun kolin jama'ar Sin na dora muhimmanci sosai a kan yadda ake hukunta laifuffukan da ke shafar tashe-tashen hankali da suka auku a birnin Tibet a ran 14 ga watan Maris na shekarar 2008 da kuma birnin Urumqi a ran 5 ga watan Yuli na shekarar da ta gabata, kuma za ta ba da jagoranci ga kotunan da abin ya shafa da su hukunta laifuffukan yadda ya kamata bisa doka.

A cikin rahotonsa kuma, shugaban babbar hukumar kula da harkokin shari'a ta jama'ar Sin, Mr.Cao Jianming ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, hukumomin kula da harkokin shari'a na Sin sun kara sa ido a kan yadda ake kashe kudaden da aka kebe domin zaman rayuwar jama'a da farfado da yankunan da girgizar kasa ta galabaitar da su, kuma sun mai da hankali a kan hukunta laifin ba da rashawa a fannin harkokin kasuwanci.

A game da ayyukan da za su gudanar a shekarar 2010, Mr.Wang Junsheng, shugaban kotun kolin jama'ar Sin ya bayyana cewa, za a inganta gyare-gyaren tsarin shari'a da tabbatar da adalci da tsabta a fannin shari'a. Sa'an nan, a cewar Cao Jianming, shugaban babbar hukumar kula da harkokin shari'a ta jama'ar Sin, za a kara horar da jami'an shari'a, tare kuma da kyautata imanin jama'a kan yadda ake gudanar da doka.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China