in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin sun ci gaba da tattaunawa da wakilan jama'ar kasar
2010-03-11 19:52:17 cri

Ran 11 ga wata, shugabannin kasar Sin sun ci gaba da tattaunawa tare da wasu wakilan jama'ar kasar Sin da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin daya bayan daya.

A lokacin da yake tattaunawa da wakilan jama'ar kasar da suka zo daga yankin Taiwan, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya jaddada bukatar inganta amincewa da juna a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan ta fuskar siyasa da hadin gwiwarsu a harkokin tattalin arziki da kara yin mu'amala ta fuskar al'adu da aikin tarbiya.

Sa'an nan kuma, a lokacin da yake tattaunawa da wakilan jama'ar kasar da suka fito daga lardin Qinghai, Li Changchun, zaunannen mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya nuna fatansa na ganin Qinghai ta yi kokarin samun sabuwar hanyar bunkasa yanki maras ci gaba bisa kimiyya.

Haka zalika, a yayin tattaunawar da ya yi tare da wakilan jama'ar kasar da suka zo daga jihar Ningxia, Li Keqiang, mataimakin firayim ministan kasar Sin ya ce, a matsayinta na wurin da aka samu kananan kabilu, tilas ne Ningxia ta ci gaba da gaggauta raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, da kara kyautata zaman rayuwar 'yan kabilu daban daban da ayyukan raya jihar, da kuma kiyaye kwanciyar hankali da jituwa a zaman al'umma.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China