Jia Yong, shugaba ne na sashen harkokin soja na kamfanin dillancin labaru na Xinhua. Ya yi nuni da cewa, a shekaru 10 ko fiye da suka wuce, a ko wadanne shekaru 2 kasar Sin ta kan kaddamar da takarda kan harkokin tsaron kasa, inda take yin karin bayani kan harkokin tsaron kasa da yadda ake bunkasa soji filla-filla, haka kuma bayanin da ta kan yi kan kudin aikin soja ya fi na dimbin kasashen duniya yawa.
Mr. Jia Yong ya kuma ci gaba da cewa, bisa kasafin kudi da kasar Sin ta kebe a aikin soja a shekarar 2010, an ce, matsakaicin kudin da ko wane mutumin Sin zai kashe a aikin soja ya kai kashi daya daga cikin kashi gomai bisa na ko wane mutumin kasar Amurka. Sa'an nan, yawan kudin da kasar Sin ta kashe a aikin soja ya kai kashi 1.4 cikin dari bisa jimillar GDP da ta samu. A yayin da matsakaicin adadi a wannan fanni a duniya ya kai kashi 2.5 zuwa 3 cikin dari.
Mr. Jia Yong ya nuna cewa, bisa ga hakikanin gaskiyar abin sannu a hankali, zargin da ake yi wa kasar Sin na cewa, za ta kawo barazana zai ci tura. (Tasallah)