in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan CPI na kasar Sin a watan Fabrairu ya karu da kashi 2.7 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara
2010-03-11 15:05:24 cri

A ran 11 ga wata, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ba da adadin cewa, hawan ma'aunin kayan da aka saya wato CPI ya karu da kashi 2.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara, kuma ya karu da kashi 1.2 cikin dari bisa na watan da ya gabata. Tun da watan Nuwamba na shekarar bara, wannan ya zama watanni hudu a jere kenan da aka samu karuwar yawan CPI.

Sheng Laiyun, kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin ya bayyana cewa, ko da yake an samu sauye-sauye a kan farashin kayayyaki a bana, amma domin ana samar da isashen kayayyakin gona, kuma yawan kayayyakin masana'an da aka samar da ake bukata ba su sauya ba, kana gwamnatoci na matakai daban daban na mai da hankali sosai kan farashin kayayyaki, sabo da haka, bisa manufofin kasar, za a tabbatar da farashin kayayyaki daga duk fannoni a bana.

Ban da haka kuma, adadin da hukumar kididdiga ta kasar ta bayar a ran 11 ga wata ya nuna cewa, a watan Janairu da Fabrairu na bana, yawan kudin da aka samu daga manyan masana'antu ya karu da kashi 20.7 cikin dari a watan Janairu da Fabrairu na bana.

Mista Sheng Laiyun ya furta cewa, a watannin biyu da suka gabata, an ci gaba da samun bunkasuwar sana'ar masana'antu da sauri a kasar Sin kamar yadda aka yi a karshen rabin shekarar bara.(Asabe)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China