in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin sun yi tattaunawa tare da wakilan jama'a
2010-03-10 20:20:54 cri

Ran 10 ga wata, a nan Beijing, shugabannin kasar Sin wato Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da dai sauransu sun yi tattaunawa tare da wasu wakilan jama'ar Sin da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

A lokacin da yake tattaunawa tare da wakilan jama'ar da suka fito daga lardin Henan, Mr. Hu Jintao ya jaddada bukatar karfafa gwiwar bangarori daban daban don samun hakikanin ci gaba ta fannin gaggauta canza hanyar raya tattalin arziki. Ya kuma kara da cewa, dole ne a tabbatar da karin amfanin gona daga dukkan fannoni da bunkasuwar aikin gona mai dorewa, da kyautata aikin gona ta fuskar yin gogayya a kasuwar duniya.

A yayin da ya yi tattaunawa da wakilan jama'ar da suka fito daga lardin Shanxi, Wu Bangguo ya bayyana cewa, wajibi ne a ci gaba da sa muhimmanci kan kafa doka a harkokin zaman al'ummar kasa, da gyara dokokin da ba su dace da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma ba cikin sauri, da kammala aikin kawar da dokoki da ka'idoji da ba su dace ba daga dukkan fannoni, da zummar tabbatar da samun tsarin dokoki na gurguzu mai sigar musaman ta kasar Sin cikin lokaci.

Bayan haka kuma, a wannan rana, Wen Jiabao ya tattauna tare da wakilan jama'ar Sin da suka zo daga lardin Hebei, inda ya furta cewa, tilas ne a rubanya kokarin sa kaimi kan kyautata tsarin masana'antu na gargajiya da kawar da ci bayan da ke tattare da ayyukan samar da kayayyaki, da gaggauta yin kwaskwarima kan fasaha da sabunta fasaha a masana'antu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China