in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma burin rage yawan hayaki mai gurbata muhalli na shekarar 2006 zuwa shekarar 2010
2010-03-10 20:10:47 cri

A ranar 10 ga wata, a nan birnin Beijing, mataimakin darekta na kwamitin yin gyare-gyare da raya kasa na kasar Sin Xie Zhenhua ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2009, kasar Sin ta rage yawan makamashin da take yin amfani da shi wajen samar da kayayyaki da kashi 14 cikin 100, yayin da yawan hayakin Oxygen da take amfani da shi wajen yin sinadarai ya ragu da kashi 10 cikin 100, kana, yawan hayakin sulphar da take fitarwa ya ragu fiye da kashi 13 cikin 100, watau ke nan kasar Sin ta cimma burin rage yawan hayaki mai gurbata muhalli da aka tanada cikin shirin samun bunkasuwa a karo na 11 na shekaru biyar-biyar kafin shekara daya kamar yadda take zato.

A wannan rana, taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a ya yi wani taron manema labaru kan harkokin tsimin makamashi da rage yawan hayaki mai gurbata yanayi.

Xie Zhenhua ya ce, majalisar wakilan jama'a ta kasar ta zartas da wannan shiri. A sakamakon haka, kasar Sin ta gina tsarin sa ido kan yawan kididdigar da take samu, kuma ta yi kokarin gudanar da shirin cikin tsanaki, kuma ta aiwatar da shirin tsimin makamashi a manyan ayyukan gine-gine 10 da suka hada da masana'antu da gine-gine da zirga-zirgar kasar, ke nan kasar Sin ta kara karfi wajen yaki da matsalar gurbata muhalli.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China