in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje koli na duniya da za a shirya a Shanghai zai zama dandali mai kyau don kasar Sin ta yi cudanya da hadin kai da kasashen duniya
2010-03-10 18:40:57 cri

Sauran kwanaki 52 a fara gudanar da babban bikin baje koli na duniya mai taken EXPO a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, abin da ya sa bikin ya zama batun da manyan kusoshin kasar Sin da wakilan jama'ar kasar suka fi tattaunawa a kai a wajen tarurruka 2 masu muhimmanci na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da na majalisa mai ba da shawara kan harkokin siyasa, da suke gudanarwa a nan birnin Beijing. Yayin da yake ba da rahoto kan aikin gwamnatin kasar, Mista Wen Jiabao, firaministan kasar Sin, ya yi alkawarin shirya bikin EXPO cikin nasara, tare da samar da damar yin cudanya da hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya don neman samun bunkasuwa tare. Sa'an nan, wasu wakilan jama'ar kasar Sin sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi, kasar Sin ta yi amfani da dandalin bikin EXPO don koyon fasahohi masu ci gaba na kasahen waje, tare da inganta mu'amala a tsakanin bangarorin 2 ta fuskar al'adu.

Madam Zhu Guoping, wata wakiliya ce ta jama'ar kasar Sin, kana tana da mukamin darektar unguwar Hong Chu da ke birnin Shanghai. Ta ce, iyalai da yawa da ke zaune a unguwarta suna neman samun izinin zaman 'iyalan bikin EXPO', wato iyalan da za su ba da hayan gidajensu domin saukar baki a lokacin bikin EXPO. Saboda haka, wasu mutanen har sun fara koyon harshen Turanci da ilimin bikin EXPO a shekarun baya, tare da fatan samun bakin da za su zo daga kasashen waje su zauna a gidajensu, kamar yadda Madam Zhu ta yi bayanin cewa, 'Mutanen Shanghai na tsammanin cewa, ta hanyar karbar baki, za a iya samun abokai da yawa, abin da ya sa su farin ciki da kuma yin alfahari.'

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China