in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani ma'aikacin diplomasiyya na Sin ya karyata zancen da aka yi cewar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka kamar wani sabon salon mulkin mallaka ne
2010-03-10 17:14:56 cri

A ran 10 ga wata a birnin Beijing, Lu Qiutian, memba na kwamitin gabatar da manufofin diplomasiyya na ma'aikatar harkokin waje ta Sin ya karyata zancen cewar, hadin gwiwa da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afirka kamar wani sabon salon mulkin mallaka ne.

A dandalin diplomasiyya na Sin, yayin da yake magana da jama'a ta yanar gizo, Lu Qiutian ya bayyana cewa, Sin ta ba da taimako tana da hada gwiwa da kasashen Afirka ba tare da sharadi ba. Kuma jama'ar Sin da jama'ar kasashen Afirka suna da dankon zumunci na dogon lokaci, kuma aminai ne. Kasar Sin tana da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka masu albarkatu da marasa albarkatu. Bugu da kari, Sin tana bunkasa hadin gwiwa tsakaninsu bisa girmama juna da samun moriyar juna cikin adalci. Wadannan jita-jitar cewa, hadin gwiwa da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afirka kamar wani sabon salon mulkin mallaka ne domin mamaye albarkatu suna da boyayyiyar manufa, ko kuma son yin haka cikin rashin fahimta.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China