in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta don tabbatar da cewa yawan kudin shiga da manoman kasar Sin za su samu zai karu da kashi 6 cikin dari a bana
2010-03-10 15:55:40 cri

A ran 10 ga wata, a birnin Beijing, Wei Chao'an, mataimakin ministan kula da harkokin noma na kasar Sin ya bayyana cewa, za a yi iyakacin kokari don tabbatar da cewa yawan kudin shiga da manoman kasar Sin za su samu zai karu da kashi 6 cikin dari a bana.

A gun taron manema labaru da aka yi a ran nan, mista Wei Chao'an ya ce, ma'aikatar kula da harkokin noma ta kasar Sin za ta dauki matakai daban daban don tabbatar da cimma burinta. Matakan da za ta dauka suna kunshe da daidaita tsarin noma da kara amfanin gona da za a samu ta hanyar bunkasa sana'o'i; da kuma ci gaba da kara kudin shiga ga manoma ta hanyoyin gina manyan ayyuka na yau da kullum da bunkasuwar kimiyya da fasahar noma da na'urorin zamani na noma; da tabbatar da manufofin da za su kawo moriya ga manoma da samar da karin hanyoyin samun kudi ga manoma; kana da ingiza harkokin gina manyan ayyuka na yau da kullum da harkokin zaman al'ummar kauyuka don kyautata sharadin samun karin kudi.

Bugu da kari, Wei Chao'an ya ce, matsakacin yawan kudin da manoma suka samu bai kai yawan kudin da mazauna birane suka samu ba. Sabo da haka, tabbatar da cewa yawan kudin da manoma za su samu zai karu da kashi 6 cikin dari hakan zai ba da tabbacin rage bambanci a tsakanin birane da kauyuka da kara kudin da manoma za su samu. (Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China