in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmin abin da zai kara saurin canza hanyar bunkasa aikin gona shi ne kara raya aikin gona na zamani
2010-03-10 15:51:57 cri

A ran 10 ga wata a birnin Beijing na Sin, mataimakin ministan aikin gona na Sin Wei Chaoan ya bayyana cewa, muhimmin abin da zai kara saurin canza hanyar bunkasa aikin gona shi ne kara saurin raya aikin gona irin na zamani, wato a bunkasa aikin gona ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha da kara ilmin ma'aikata da kuma kyautata tsarin kulawa.

A wannan rana, a gun wani taron manema labaru na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Wei Chaoan ya furta cewa, domin kara karfin samun amfanin gona, kamata ya yi a kara saurin kafa tsarin tabbatar da ingancin abinci da tsarin aikin gona na zamani, da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da dai sauransu, a kokarin bunkasa aikin gona na zamani.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China