in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zama na biyu na kusoshin taron wakilan jama'ar kasar Sin
2010-03-09 21:32:54 cri

A ran 9 ga wata, an yi cikakken zama na biyu na kusoshin taron wakilan jama'ar kasar Sin, kuma jagoran kusoshin, Mr.Wu Bangguo shi ne ya shugabanci taron.

Daga ran 5 zuwa 6 ga wata, tawagogin wakilan jama'a da suka zo daga larduna daban daban sun yi nazari a kan rahoton gwamnati, wadanda suka nuna babban yabo a kan rahoton, tare kuma da nuna cikakkiyar amincewa kan yadda majalisar gudanarwa ta kasar ta gudanar da aikinta cikin shekarar da ta gabata. Bayan haka, wakilan sun nuna amincewa ga babbar manufa da shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma da kuma manyan fannoni 8 da za a gudanar da aiki a kai da aka gabatar cikin rahoton, kuma suna ganin cewa, ana iya cimma shirin da aka tsara bisa kara yin kokari.

Bayan haka, wakilan sun kuma gabatar da wasu shawarwari, kuma bisa shawarwarin, majalisar gudanarwa ta Sin ta yi gyare-gyare har 15 kan rahoton aikin gwamnati.

A ran 7 ga wata, tawagogin wakilai sun yi nazari a kan rahoton shirye-shirye da daftarin shirye-shirye da rahoton kasafin kudi da daftarin kasafin kudi. A ran 8 ga wata kuma, tawagogin sun yi nazari a kan daftarin gyararriyar dokar zabe. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China