in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar NPC ya yi shelar tabbatar da samun tsarin dokoki da ke da sigar musamman ta Sin cikin wannan shekara
2010-03-09 21:02:51 cri

A ran 9 ga wata, an yi cikakken zama na uku na taron shekara shekara na wakilan jama'ar kasar Sin, inda shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC), Mr.Wu Bangguo ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da samun tsarin dokoki da ke da sigar musamman ta Sin cikin wannan shekara.

A yayin da yake bayani a kan aikin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya ce, tabbatar da samun tsarin dokoki da ke da sigar musamman ta Sin cikin shekarar 2010 aiki ne da ya fi muhimmanci ta fannin kafa doka a wannan shekara, haka kuma ya kasance aiki mai matukar muhimmanci ga majalisar wakilan jama'ar Sin a shekarar.

Mr.Wu Bangguo ya ce, ya kamata a gaggauta yin dokokin da za su kasance ginshikai cikin tsarin dokoki a yayin da ake kyautata ingancin dokokin, kuma a gyara dokokin da ba su dace da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma ba tun da wuri, a ci gaba da inganta dokokin da ke shafar zaman al'umma.

Mr.Wu Bangguo ya kuma kara da cewa, ya kamata a kara sa hannun jama'a wajen ayyukan kafa doka, a saurari ra'ayoyi na bangarori daban daban, musamman na talakawa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China