in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na ketare sun mai da hankali kan kasar Sin sosai
2010-03-09 20:48:35 cri

A kwanan baya, matakai da dama da Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya gabatar game da yin gyare-gyare kan tattalin arziki a cikin rahoton ayyukan gwamnatin kasa sun jawo hankalin kafofin yada labaru na kasashen waje matuka.

Jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan ta ba da sharhi cewa, tilas ne kasar Sin ta mai da hankali kan raya tattalin arziki ta hanyar da ke dacewa. Ga alama yin gyare-gyare kan tsarin rarraba kudin shiga shi ne batu mafi muhimmanci a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, a cikin sharhinta, jaridar Nouvelles d'Europe ta kasar Faransa tana ganin cewa, abun da manyan jami'an kasar Sin suka sa muhimmanci a kai shi ne yin kokarin raya kasa ta hanyar kimiyya tare da mayar da al'amuran da suka shafai jama'a a gaba da kome, a maimakon neman bunkasa tattalin arziki kawai. Gwamnatin Sin tana kokarin gyara manyan tsare-tsarenta ta fannin mulkin kasa daga wadatar da kasa zuwa wadatar da jama'a.

Haka zalika, ba za a samu bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa yadda ya kamata ba, sai an gyara tsarin siyasa. Kafofin yada labaru na ketare su ma sun sa muhimmanci kan bayanin da Mr. Wen Jiabao ya yi game da yin gyare-gyare kan tsarin siyasa a cikin rahoton ayyukan gwamnatin. Kamfanin dillancin labaru na Associated Press na kasar Amurka ya furta cewa, bisa abubuwan da aka tanada cikin daftarin dokar zabe da ake tattaunawa, an ce, za a nuna adalci a tsakanin mazauna birane da kuma wadanda ke zaune a yankunan karkara a fannin zaben wakilan jama'a. Haka ya kasance wani bangare ne na sabon kokarin da kasar Sin ke yi da zummar rage gibi a tsakanin birane da yankunan karkara a harkokin bunkasuwa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China