in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe kudin Sin fiye da yuan miliyan 690 domin yaki da bala'in dusar kankara a jihar Xinjiang
2010-03-09 18:40:59 cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar, an ce, bala'in dusar kankarar da ya yi ta abkuwa tun daga lokacin hunturu na shekarar da ta wuce har zuwa yanzu ya haddasa babbar asara a jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Kawo yanzu gwamnatin Sin ta zuba kudin da ya kai yuan miliyan 690 ko fiye domin taimakawa masu fama da bala'in wajen farfado da zaman rayuwa da aikin ci gaban jihar yadda ya kamata.

Qian Zhi, mataimakin shugaban jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, baya ga ba da kudin yaki da bala'in, gwamnatin tsakiya ta kasar da hukumar jihar sun yi jigilar dimbin ciyayi da abincin dabbobi da tufafin kare sanyi da barguna cikin gaggawa, ta haka an ba da tabbaci ga zaman rayuwar masu fama da bala'in da gudanar da ayyukansu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China