in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin inganta masana'antu tare da canja hanyoyin bunkasuwar tattalin arziki
2010-03-09 18:39:07 cri

A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin da ake gudanarwa, firaminista Wen Jiabao ya bayar da rahoto game da aikin gwamnati cewa, shekara ce 2010 shekara mafi muhimmanci wajen "ci gaba da magance matsalar hada-hadar kudi, da bunkasa tattalin arziki cikin sauri yadda ya kamata, tare da sa kaimi ga yunkurin canza hanyoyin raya tattalin arziki". Bayanin Wen Jiabao ya sami goyon baya sosai, wasu wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin daga sana'o'in tattalin arziki sun ce, inganta masana'antu shi ne wani muhimmin aiki na yunkurin canja hanyoyin raya tattalin arziki, yanzu ana kokarin inganta masana'antun gargajiya, kuma sannu a hankali za a kyautata masana'antun da ba su gurbata muhalli, wannan zai kafa tushe ga bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa na kasar Sin.

A karshen shekarar 2008, matsalar hada-hadar kudi ta duniya, ta yi mummunar illa ga masana'antun karafa amma ba na bakin karfe ba, sai a shekarar 2009, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "shirin ingantawa da raya masana'antun samar da karafa". Game da haka, Mr. Li Peixing shugaban wani kamfani mai samar da karafa da ke jihar Gansu yana ganin cewa, ko da yake yanzu tasirin matsalar hada-hadar kudi yana karewa, amma ya kamata a ci gaba da inganta masana'antun karafa. Ya ce, "A galibi dai, masana'antun sarafa suna da kyakkyawar makoma, yawan bukatun da ake da su a ko wace shekara yana karuwa da kashi 10 zuwa 20 cikin kashi 100. amma yanzu kasar Sin tana fuskantar matsalar karancin ma'adinai, da matsalar gurbata muhalli. Sakamakon haka, inganta masana'antun karafa yana da muhimmanci sosai."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China