in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar gyara dokar zabe domin bunkasa siyasar dimokuradiyya
2010-03-09 16:51:08 cri

A ran 9 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya bayyana cewa, gyara dokar zabe da kyautata tsarin zabe na zaman gurguzu mai siffar musamman na kasar Sin muhimmin aiki ne da za a yi domin kyautata tsarin majalisar wakilan jama'a da bunkasa siyasar dimokuradiyya ta zaman gurguzu.

A wannan rana da yamma, an yi cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jama'a ta shekara-shekara. Inda Wu Bangguo ya ba da rahoton aiki a madadin zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

Wu Bangguo ya ce, an dudduba daftarin dokar zabe a gun taron zaunanen kwamiti da aka yi a watan Oktoba na shekarar 2009, sannan kuma an bayar da shi a internet don saurarar ra'ayoyin jama'ar da suka zo daga bangarori daban daban. Kana a watan Disamba na shekarar bara, zaunanen kwamitin ya sake tattauna kan daftarin, kuma an yanke shawarar sake dudduba daftarin a gun wannan taron da aka yi a ran 9 ga wata. Membobin zaunanen kwamitin suna ganin cewa, gyara dokar zabe ya dace da yanayin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, ya dace da ra'ayin jama'ar Sin, kana zai kawo moriyar raya dimokuradiyya ta kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China