in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da samun kudaden musaya da aka tanada a kasar Sin yayin da ake fama da matsalar kudi ta duniya
2010-03-09 15:31:44 cri

A ran 9 ga wata, a birnin Beijing, Yi Gang, mataimakin gwamnan bankin jama'ar kasar Sin kuma shugaban hukumar kula da harkokin kudaden musaya ta kasar Sin ya bayyana cewa, a yayin da ake fama da matsalar kudi ta duniya a shekarar 2008 da ta 2009, ban da tabbatar da samun kudaden musaya kamar yadda aka yi a da, har ma an samu moriya kan haka.

Bugu da kari, Mista Yi Gang ya ce, muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka na kula da harkokin kudaden musaya shi ne ware jari da kyau, da jaddada rage rikicin da za a yi fama da shi. A kan batun zuba jari, kasar Sin ba ta zuba jari kan ba da jinginan gidaje da dai sauransu. Yi Gang ya jaddada cewa, muhimmin aikin da hukumomin kula da kudaden musaya suka yi shi ne rigakafin rikici.

Dadin dadawa, Mista Yi Gang ya furta cewa, ba a fatan ganin cewa, za a mai da aikin zuba jari kan kasuwar sayen bashin Amurka ya zama aikin siyasa. Ya ce, aikin sayen bashin Amurka da sayar da shi shi ne aikin zuba jari bisa tsarin kasuwanci. Ba a son a mai da shi ya zama aikin siyasa. Kasar Sin ita ce mai zuba jari da za ta dauke nauyinta. Yayin da ake zuba jari, za a samu moriya a tsakanin bangarorin biyu.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China