in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun mai da hankali a kan manufar diplomasiyya ta kasar Sin
2010-03-09 09:35:06 cri

A gun taron manema labaru na babban taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 da aka shirya a ran 7 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya amsa tambayoyi da manema labaru na gida da na kasashen waje suka yi masa dangane da manufar diplomasiyya da dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen waje. Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun mai da hankalinsu a kan amsar da Yang Jiechi ya ba da.

Bisa labarin da Internet na kamfanin BBC na kasar Britaniya ya bayar, an ce, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, Sin da Rasha sun kafa abin misali game da dangantaka tsakaninsu musamman tsakanin manyan kasashe, wannan ya sha bamban da maganar da ya yi dangane da dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka.

Bisa labarin da aka bayar, bayan abkuwar halin zafi wajen dangatakar da ke tsakanin Sin da Amurka, makon jiya, gwamnatin Amurka ta aika zaunanen mataimakin ministan harkokin waje James Steinberg da babban darektan ofishin tsaro na fadar shugaba wato White House mai kula da harkokin Asiya Jeffrey Bade zuwa kasar Sin don inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na AP ya bayar, an ce, batutuwan kasar Amurka na sayar wa yankin Taiwan makamai da ganawar da Dalai da shugaban Amurka su ne sanadiyar tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. A ganin kasar Sin, ingantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ya dogara ga ra'ayin Amurka. Jaridar Wall Street da jaridar New Yorks Times sun ruwaito labarin da kamfanin AP ya bayar.Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na AFP na kasar Faransa ya bayar, an ce, a ganin kasar Sin, kasar Amurka ta kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, amma kasar Sin ta yi kira ga manyan kasashen biyu da ke shiyyar tekun Pasific da su yi kokari tare don mayar da dangantakar dake tsakaninsu kamar yadda ya kamata. A cikin labarin, an kara da cewa, kasar Sin ta jaddada cewar Sin da kasashen Afirka suna yin hadin gwiwa bisa ka'idar samun moriyar juna, kuma Sin tana ba da taimako ga kasashen Afirka wajen gina manyan ayyukan yau da kullum.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China