A gun taron manema labarun da aka yi a ran nan, Musa Ecweru, ministan kula da harkokin yaki da bala'i na kasar Uganda ya bayyana cewa, a sakamakon abkuwar bala'in gangarar baraguzun duwatsu tare da malalar laka a yankin duwatsu, kuma ba a gina hanya a yankin, shi ya sa, ake gudanar da aikin ceto sannu a hankali. Gwamnatin kasar ta yi kira ga kasashen dake abuta da ita wajen samun bunkasuwa tare da hukumomin M.D.D. da su tura wani babban jirgin saman mai yin jigila don kai motoci zuwa yankin dake fama da bala'in, ta yadda za a ingiza gudanar da aikin cigiyar gawawwaki.
Ya zuwa ran 8 ga wata, masu aikin ceto sun gano gawawwaki 83 daga buraguza, amma mutane kimanin 350 sun bata, kuma mai yiyuwa ne suka mutu.(Asabe)