in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kwaskwarima kan dokar zabe da zummar tabbatar da daidai wa daida
2010-03-08 18:25:28 cri

A wajen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake gudanarwa, ana yin wani babban aiki na musamman, wato yin tattaunawa kan shirin kudurin da aka samar don neman gyara dokar zaben kasar. A ranar 8 ga wata, wakilan jama'ar kasar Sin kimanin 3000 sun saurari bayanin da Wang Zhaoguo, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya yi game da shirin kudurin. Sa'an nan burin da ake neman cimmawa wajen aiwatar da gyaran shi ne don tabbatar da adalci a tsakanin mazauna birane da masu zama cikin kauyuka, a lokacin da suke kada kuri'ar zaben wakilan jama'a, ta yadda za a samu damar kara kyautata tsarin zaben kasar.

An tsara dokar zaben kasar Sin shekaru 57 da suka wuce, wadda aka taba yin kwaskwarima a kanta har sau 5. Sai dai gyarawar da za a yi a wannan karo ta fi muhimmanci, domin ta shafi rabin shadarun da ke cikin kundin dokar. Sa'an nan, Wang Zhaoguo ya bayyana manufar da ta fi muhimmanci da cewa, 'Za a nuna adalci tsakanin mazauna birane da masu zama cikin kauyuka kan ayyukansu na jefa kuri'a don zaben wakilan jama'a, sa'an nan za a tabbatar da cewa ko wane yanki, ko wace kabila, ko wane sashi za su samu wakilansu gwarwadon yawan al'umma.'

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China